<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>A Cikin Farko Allahnmu LW347</title>
<lyrics>[V1]
 1) A cikin farko Allahnmu
 Ya hallici dukan abu
 Cikin sama da akan duniya
 Dukan abin da kyau.

[V2]
 2) Ya hallici su mutane
 Su Adamu, da Hawa'u
 Ya sa su cikin gona ta Aidin
 Su aikace ta kuwa.

[V3]
 3) Ya dokace su Adamu
 Su Hawa'u kada su ci
 Daga icce na tsakar gona
 Ko mutuwa za su yi.

[V4]
 4) Shaiɗan ya shiga gonar nan
 Ya jarabci Hawa'u dai
 Ya sa ta shakkar maganar Allah
 Ta bi maganarsa.

[V5]
 5) Ta ɗiba ɗiyan iccen nan.
 Ashe, ta ci, ta ba miji
 Sun ɓoye daga murya ta Allah
 Sabo da tsoronsa.

[V6]
 6) Allah ya yi masu horo
 Ga maciji, la'ananne ne shi
 Mace ta haifa da baƙinciki
 Wahala tata ce.

[V7]
 7) Da zufa bisa fuskarka
 Ya Adamu, ka ci abincinka
 Ҡasa ta haifi ƙayayuwa kuma
 Zan kore ku da nan.

[V8]
 8) Allah ya kashe ɗan rago
 Da fatarsa ya rufe wofinsu
 Ya faɗa masu akwai Mai Zuwa
 Mai Ɗauken laifofi.

[V9]
 9) Mun gaji halin Adamu
 Duk mutane na duniya
 Amma ya aiko Yesu Mai Ceto
 Kama da ɗan rago.

[V10]
 10) An kashe Yesu Ɗan Allah
 Da jininsa ya kwashe laifina
 Yanzu na zama ta Allah kuma
 Ta wurin bangaskiya.

[V11]
 11) Na gode maka ya Allah
 Don ƙamnarka, don gafara
 Ka taimake ni, in bi ka kullum.
 Da zuciya ɗaya fa, Allahna.</lyrics>
<hymn_number>347</hymn_number>
</song>